Abdulrasheed Bawa ya fara aiki EFCC ne a matsayin Mataimakin Sufeto (ADS) a shekarar 2004. A watan Oktoban 2015 ne aka naɗa shi ya jagoranci binciken hukumar kan Diezani Alison-Madueke, tsohuwar ministar albarkatun man fetur da kuma mukarrabanta. An naɗa Bawa a matsayin shugaban EFCC a ranar 16 ga Fabrairu 2021, kuma a ranar 24 ga Fabrairu 2021 majalisar dokoki ta kasa ta tabbatar da shi a matsayin. Ya karbi ragamar hukumar ne daga hannun, Ibrahim Magu, tsohon shugaban riko na hukumar wanda shi ma a dakatar da shi bisa zargin rashawa. AbdulRasheed Bawa shi ne shugaban hukumar mafi ƙarancin shekaru.

Post a Comment

0 Comments