Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya nada Abdulkarim Chukko a matsayin shugaban riko na hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa. An nada shi ne kwana guda bayan dakatar da shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa wanda a yanzu haka yake hannun hukumar tsaro ta DSS bisa binciken da ake yi kan ayyukan ofishinsa. Kafin nadin nasa, Abdulkarim Chukko shi ne daraktan gudanarwa na EFCC kuma yana cikin ma'aikatan da suka soma aiki a hukumar.

Post a Comment

0 Comments