Kungiyar Kasashen Yammacin Africa (ECOWAS) #BBChausa

Kungiyar ECOWAS ta umarci Sojojin Nijar su gaggauta mika mulki cikin mako guda.

Wannan na cikin abubuwan da kungiyar ECOWAS ta cimma matsaya kan juyin mulki a Nijar a zaman ta na Lahadin nan.

1) Baiwa jagororin juyin mulkin umarnin mika mulki cikin mako guda

2) Takunkumin hana tafiye tafiye ga dakarun da suka jagoranci juyin mulki a kasar

3) Rashin nuna goyon baya kan tursasa shugaba Bazoum ya ajiye mulki

4) Watsi da dakarun soji na kasashen waje dake nuna goyon baya ga juyin mulki a kasar

5) Takunkumi kan tattalin arziki

6) Takunkumin hana zirga-zirgar jiragen sama #Hausa #BBChausa 

Post a Comment

0 Comments