@Hausa Tsohon Sarkin Kano Ya Gana Da shugaban kasar Nijar

🇳🇪/🇳🇬 A daidai lokacin da wakilan kungiyar africa ta AU da ECOWAS basu sami damar  ganawa da Shugaban soji na Nijar ba. Sarkin Kano na 14, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya samu ganawa da Shugaban mulkin soji na Jamhuriyyar Nijar da suka hambarar da mulkin zababben Shugaban kasar Muhammad Bazoum a kwanakin baya-bayan nan. 

Khalifan na Tijjaniyyya kuma tsohon gwamnan babban banki na Najeriya CBN, ya samu ganawa da Shugaban sojin ne a ranar Larabar 9 ga watan Agustan 2023. 

📸-Khalifah Sanusi

Post a Comment

0 Comments