Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya mayar da Hukumar Alhazai da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta NEMA karkashin ofishin Mataimakin Shugaban Kasa. Shugaban kasar ya kuma amince da samar da tsari a hukumance na yadda za a dinga tafiyar da Ofishin Mataimakin Shugaban Kasar tare da ba shi mataimaka na musamman kan sha'anin mulki da za su yi aiki tare da Mataimakin Shugaban Kasar wajen gudanar da ayyukansa.

Post a Comment

0 Comments