Tarayyar Najeriya ya tanada. Ƙarin naɗe-naɗen su ne: Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kuma naɗa Hadiza Bala Usman a mataimakiya ta musamman a kan ayyukan daidaita manufofi. Hannatu Musan Musawa kuwa, ya naɗa ta matsayin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin al'adu da bunƙasa harkokin nishaɗantarwa. Haka kuma, Shugaba Tinubu ya naɗa Sanata Abdullahi Abubakar Gumel a muƙamin babban mataimaki na musamman kan harkar Majalisar Dattijai. Yayin da Hon. Olarewaju Kunle Ibrahim ya kasance babban mataimaki na musamman kan harkar Majalisar Wakilai. Sai kuma, Adeniyi Bashir Adewale, mutumin da Shugaba Tinubu ya naɗa kan muƙamin Babban Kwamturola na riƙa a hukumar hana fasa-ƙwauri ta Najeriya (Customs).

Post a Comment

0 Comments